IMF: Tattalin arzikin Afirka na tangal-tangal
April 15, 2021Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, ya ce tattalin arzikin kasashen Afirka bakar fata zai ci gaba da tafiyar hawainiya fiye da duk wata nahiya a duniya, har zuwa wani lokacin a wannan shekara saboda matsaloli masu nasaba da annobar corona.
A saboda hakan ne asusun na duniya, ke kiran kasashe masu arziki su shirya daafa wa kasashen na Afirka, musamman ta hanyoyin da za su iya samun alluran rigakafin corona cikin sauki.
A cewar IMF din, tattalin arzikin kasashen bakar fata, na kokari ne na farfadowa daga suma da suka yi musamman daga bara i zuwa bana, inda aka samun karuin mutum miliyan 32 da suka fada cikin hali na fatara mai muni.
Kasashen Afirka 17 a cewar asusun na IMF, na cikin garari na nauyin basukan da manyan bankunan duniya ke bin su, da ma karuwar wadanda suka rasa abin yi daga bara zuwa banan.