India da Pakistan sun cimma yarjejeniya kan makamin nukiliya
February 21, 2007Talla
Kasashen India da Pakistan sun rattaba hannu kann yarjejeniyar kauce yin amfani da makamin nukiliya a tsakanin juna.
An dai gudanar da sa hannun ne a birnin New Delhi na kasar India, a tsakanin ministan harkokin wajen Pakistan, Khurshid Kasuri da takwaran sa na India Pranab Mukherjee.
Ya zuwa yanzu dai babu bayani na abubuwan da wannan yarjejeniya ta kun sa, ballantana kuma yadda za´a aiwatar da yarjejeniyar.
A gefen wannan yarjejeniya, ministocin biyu sun kuma tattauna batu na ayyukan ta´addanci, da a yanzu haka ke ciwa kasashen biyu tuwo a kwarya.