1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

India da Pakistan sun shirya kaddamar da shirin kafa bututun gas tsakaninsu

April 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0B

Kasashen Iran da Pakistan,sun sha alwashin yin aiki tare akan wani shiri na shimfida bututun iskar gas,idan har kasar India taki shiga wannan shiri.

Tun farko shirin wanda zai ci dala biliyan 7,zaa shinfida bututun da zai rika kai iskar gas daga Iran yabi ta cikin Pakaistan zuwa India,kuma jamiai sunce zasu sanya hannu akan yarjejeniyar a watan yuni mai zuwa.

Kasar Amurka dai wadda take ganin Iran tana kokarin kera makaman nukiliya ne,ta bukaci Pakistan da India da kada suyi huldar kasuwanci da Iran,maimakon haka gwamnatin Amurkan ta bukace su da suyi kokarin kan wani shirin na shimfida bututun iskar gas din wanda zai ratsa ta cikin Afghanistan daga Turkmenistan .

Tun da farko kasar Amurka tayi tayin bada taimakon fasahar nukiliya ga kasar India,domin inganta tattalin arzikinta mai tasowa,amma taki yin irin wannan tayi ga kasar Pakistan,saboda a cewarta rawa da wani dan kasar ta Pakistan ya taka,wajen sayarda bayanan asiran nukiliya ga kasashen Iran,Libya da Koriya ta arewa.