1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChaina

Indiya da Chaina sun nemi karfafa dangantaka

Abdullahi Tanko Bala
October 23, 2024

Firaministan India Narendra Modi da takwaransa na Chaina Xi Jinping sun gana gaba da gaba a karon farko a daura da taron kolin BRICS a Rasha bayan tsamin dangantakar da ta haifar da arangama a kan iyakokinsu a 2020

https://p.dw.com/p/4m9p0
Shugaba Modi na Indiya da Shugaba Xi na Chaina
Hoto: China Daily/REUTERS

Firaministan Indiya Narendra Modi da takwaransa na Chaina Xi Jinping sun gana a daura da taron kolin shugabannin kasashen kungiyar BRICS da ke gudana a Rasha 

Ganawar ta biyo bayan yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma ne a makon da ya gabata na tsaron kan iyakokinsu shekaru hudu bayan wata arangama da suka yi da ta haifar da rashin jituwa a tsakaninsu.

Sojojin Indiya da na Chaina sun yi artabu a fada mafi muni a 2020 da aka dade ba a ga irinsa ba cikin gomman shekaru

Kasashen biyu sun jibge dubban sojoji a kan iyakar da suke takaddama a arewacin lardin Ladakh sakamakon rikicin.