Zanga-zangar Indiya ta lashe rayuka
February 26, 2020Talla
Firaministan Indiyan, Narendra Modi ya bukaci al'ummar kasar da su kwantar da hankula a kan boren da ke ci gaba da daukar sabon salo. Wannan dai shi ne bore mafi muni da birnin na New Delhi ke fuskanta, a dangane da haka ne ma Mr Modi ya bukaci sojoji da su saka dokar hana fita a birnin.
Tun a watan Disambar shekarar da ta gabata ne al'ummar kasar ta Indiya ke boren adawa da sabuwar dokar dan kasa, inda suke ta dauki-ba-dadi da jami'an tsaro. Musulmi da dama ne wannan rikicin ya tilsata musu barin gidajensu yayin da aka kona wasu masallatai a birnin na New Delhi.