1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan tsaron Indonesiya na murmurewa

Abdul-raheem Hassan
October 11, 2019

Rundunar 'yan sanda a Jakarta ta baza koma na kama sauran maharan da ke da hannu a cakawa ministan tsaron kasar Wiranto wuka a ciki.

https://p.dw.com/p/3R6jh
Selbstmordanschlag in Surabaya Indonesien
Hoto: Getty Images/AFP/J. Kriswanto

Binciken 'yan sanda ya tabbatar da mahara biyu da suka soki ministan na da alaka da kungiyar IS. Ministan tsaron Wiranto mai shekaru 72 ya gamu da wannan ibtila'i yayin da yake sauka daga motarsa.

Wannan harin ya faru ne gabannin fara wa'adin mulki na biyu na shugaba Joko Widodo. Yanzu haka ministan ya fara samun sauki a gadon asibiti.