1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC ta jaddada gudanar da zabe a Febrairu

Zainab Mohammed Abubakar
January 17, 2023

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ya ce, ba za a dage zaben shugaban kasa da aka tsayar da gudanarwa a watan gobe ba, duk da karuwar matsalolin rashin tsaro.

https://p.dw.com/p/4ML9K
Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Da ya ke magana a cibiyar nazarin siyasa da manufofin kasashen duniya ta Chatham da ke London, Mahmood Yakubu ya ce, INEC ta shirya tsap, domin gudanar da zabe mai nagarta a wannan kasa ta Afirka da ta fi kowacce yawan al'umma, duk da tarin kalubalen da ke gabanta.

Najeriyar mai yawan al'umma sama da miliyan 200, kuma mafi karfin tattalin arziki a Afirka, na fama da matsalolin masu tada kayar baya a yankin arewa maso gabashi, rikicin kuma da ya yadu zuwa sauran sassan kasar.

A ranar 25 ga watan Febrairu ne ‘yan Najeriya za su zabi sabon shugaban kasa, zaben da ka iya yin tasiri a fadin nahiyar.