INEC ta dakatar da kwamshinan zaben jihar Adamawa
April 17, 2023Har ya zuwa yammacin yau dai babu keyar Hudu-Arin a hedikwatar hukumar zaben balle kokari na wanke suna bisa ayyana sakamakon zaben jihar Adamawar tun ma kafin a kammala shi.
To sai dai kuma wata sanarwa ta hukumar zaben ta ayyana dakatar da kwamishin daga alakanta kansa da harkoin zaben balle kaiwa ya zuwa kusantar ofishin hukumar da ke a birnin Yola.
Sanarwar da ke da sa hannun sakatariya ta hukumar ta kasa Rose Anthony dai kuma a fadar kakaki ta hukumar Zainab Aminu, ta kuma umarci sakataren mulki na hukumar reshen Adamawa da ya ci gaba da jagorantar harkokin ofishin har illa ma sha Allahu.
Har ya zuwa yanzu dai Hudu-Arin ya yi batan dabo tun bayan sanar da sakamakon da ya ta da hakarkari cikin fagen siyasar Tarrayar Najeriyar.
Matakin na kwamishinan zabe Hudu Yunusa Ari na aiyyana Aishatu Dahiru ta jam'iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben dai ya kai ga damuwa mai girma cikin jihar in da magoya bayan jam'iyyar PDP suka share daukacin ranar yau suna zanga-zanagr neman ayyana dan takararsu kuma gwamnan jihar Ahmadu Fintiri a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben.
Ko bayan zargin rabon kudi dama amfani da daba dai rikicin zaben Adamawar na neman rikidewa ya zuwa batu na kabilanci cikin jihar da ke fuskantar barazar rabewa yanzu.
Aishatu Binanin dai na samun goyon baya na kabila ta Fulani a yayin kuma da Fintarin ke da tagomashi a ragowa na kabilu na jihar. Tarrayar Najeriyar dai ta saba ganin ayyana sakamakon zabe tun ma kafin a kammala shi. Hasali ma dai shi kansa sakamakon zabe na shugaban kasar a shekara ta 2007 ya bayyana ne da jihohi 16 maimakon 36 a zamani na tssoho na shugaba na hukumar zabe ta kasar Muarice Iwu.
To sai dai kuma gyaran dokar zabe ta kasar kuma a tunanin Barrister Buhari Yusuf, ya sada kamar wuya na gaban kai a cikin tsarin da ya fayyace ayyuka na jami'ai na hukumar INEC. Duk da cewar dai INEC din ta ayanna sanar da sakamkon a matsayin aikin baban giwa, akwai tsoron rikicin na iya komawa ya zuwa zauren kotuna da ke da jan aikin fassara bisa makomar sakamakon.
To sai dai kuma a fadar Barrister Mohamed Saidu Tudun wada da ke zaman wani lauya mai zaman kansa , Hudu Arin na iya share watanni dai-dai har 36 cikin gidan maza sakamako na kokarin shiga sharo ya kuma san ba shi da shanu.