Inganta hakar ma'adanai a Jamhuriyar Nijar
January 8, 2014A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin farar hula masu saka ido cikin aikin hakar ma'adanai a kasar ne, suka soma nuna fushi dangane da yadda suka ce gwamnatin kasar da shugabannin Kamfanin AREVA suka gudanar da tattaunawa ta tsawon kwanaki biyu a birnin Yamai a asirce, da kammalawa ba tare da yi wa 'yan kasa bayani a kan sakamakon da suka cimma ba.
Gwamnatin kasar da kampanin sun shafe kwanaki biyu suna tattaunawa a birnin na Yamai a wani mataki na shawo kan sabanin da yake da akwai tsakanin bangarorin biyu, dangane da tsarin da ya kamata su ci gaba da aiki a kai tun bayan da tsohuwar yarjejeniyar da ta hada bangarorin biyu ta kawo karshe makon jiya daya.
Tun ranar Litanin da ta gabata wata tawagar shugabannin Kamfanin na AREVA a karkashin jagorancin mataimakin babban daraktan wannan kampani wato Olivier Wantz ta isa birnin na Yamai inda ta hau tebirin tattaunawa da gwamnatin kasar ta Nijar karkashin jagorancin ministan ma'adanai na kasa Malama Ladan Cana. Amma ba yadda ta saba kasancewa a baya zaman da bangarorin biyu suka yi a ofishin ministan ma'adanai na kasa ya wakana ba tare da 'yan jarida hatta na kafofin yada labaran gwamnati balantana masu zaman kansu.
Kungiyar GREEN da ke fafutkar saka ido cikin tafiyar da aikin hakar ma'adanai ta nuna damuwa a game da yadda gwamnati da AREVA suka kara wa 'yan kasa labule. Kuma ta ce yanzu haka tana da fargabar yiwuwar an ci da gumin kasar Nijar cikin wannan zama cewar Soly Ramatu.
Kokarin jin ta bakin ministan ma'adanai ko wani babban jami'in ma'aikatar kan wanann batu ya ci tura. Amma yanzu haka kungiyoyin fararen hula na kasar sun kira wani taron gaggawa domin duba hanyoyin da za su tunkari wannan lamari.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Suleiman Babayo