Senegal za ta fafata da Ingila a matakin gaba
November 30, 2022Amirka da Ingila sun samu damar kai wa matakin gaba a gasar neman cin kofin kwallon kafa ta duniya da kasar Katar take daukan nauyi, yayin da aka shiga matakin tankade da reraya. Ita dai Amirka ta kai matakin wuce runukin bayan doke kasar Iran da ci 1 mai ban haushi, inda ya zama ta biyu a rukuinin kana Ingila ta doke Wales 3 da 0. Ingaila ce ta farko a rukunin inda aka cire Wales da Iran.
Tun farko dai kasashen Senegal da Netherlands sun samu nasarar wucewa zuwa makin gaba bayan da Senegal ta doke Eduador 2 da 1, ita kuma Netherlands ta doke Katar 2 da 0.
A wannan Laraba ake ci gaba da tantance kasashen, inda Tunisiya za ta fafata da Fraansa, kana Asutraliya da Denmark a rukunin D. Sannan daga bisani a rukunin C, kasashen Poland da Ajentina za su kece raini ita kuma Saudiyya da Mexiko.
Kasar Sengal wakilyar Afirka ta farko da ta kai matakin gaba za ta fafata da Ingila ranar Lahadi mai zuwa 4 ga watan gobe na Disamba.