1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki na neman kwato Falluja daga hannun IS

Zainab Mohammed/GATMay 30, 2016

Da sanyin safiyar wannan Litinin din dakarun Iraki tare da goyon bayan takwarorinsu na kasa da kasa suka kutsa garin Falluja a kokarin kwato shi daga hannun mayakan IS.

https://p.dw.com/p/1IxC9
Irak Falludscha Irakische Armee Artillerie
Hoto: Reuters/A. Al-Marjani

Mako guda kenan ake fafatawa da mayakan na IS, inda a farko aka mayar da hankali wajen kokarin ceto kauyuka da ke kewayen Falluja mai tazarar kilomita 50 daga yammacin birinin Bagadaza.

An dauki tsawon lokaci dai ana kokarin 'yanto wadannan garuruwa da mayakan na sakai suka kwace, kuma ke cin karensu babu babbaka a cikinsu. Akwai fararen hula wajen dubu 50 da wannan yaki ya ritsa da su cikin garin na Falluja. Sojojin Irakin dai sun cimma nasarar kutsawa cikin yankin daga bangarori guda uku, sai dai har yanzu suna kaffa-kaffa da kai wa 'yan IS din hari kai tsaye a cewar shugaban mayakan BADR da ke da goyon bayan Iran Hadi al-Amiri:

"Daya daga cikin mishkilolin da muke samu wajen afka wa Falluja kai tsaye shi ne halin da fararen hula za su iya tsintar kansu ciki, domin suna bukatar kariya. Mun yi kira garesu da su fice daga cikin garin domin bamu damar afka wa 'yan IS. Saboda haka ne muka jinkirta kutsawa garin na tsawon kwanaki, domin mutane su samu sukunin tserewa da rayukansu".

To sai dai a cewar kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Melissa Fleming, mutane kalilan ne suka cimma iya tserewa daga Falluja cikin 'yan kwanakinnan idan aka kwatanta da wadanda ke garin:

Irak Fallujah Soldaten beim Vormarsch
Hoto: Getty Images/AFP/Ahmad Al-Rubaye

"A cikin Falluja, mun samu rahotannin cigaban zartar da hukuncin kisa a kan maza manya da yara matasa, saboda sun ki hadewa a kungiyar ta IS. Wasu rahotanni na nuni da cewar, idan an kamaka kana kokarin tserewa daga garin za'a maka hukuncin bulala kafin a kasheka. A kan haka ne muke ganin ya dace a bude wasu hanyoyi da za su bawa jama'a damar ficewa daga birnin cikin kariya, domin kare karin asarar rayuka".

Tsawon watanni kenan mazauna garin na Falluja ke cikin halin ni 'yasu a karkashin ikon mayakan sakai da suka kwace madafan ikonsa. Baya ga tsoron hare-hare akwai matsalar rashin abinci da kayan masarufi da fargaba. Layla daya ce daga cikin iyalai kalilan da suka cimma nasarar tserewa daga Falluja kuma ke samun tallafin abinci daga hukumomin bada agaji:

Irak Militäroperation gegen IS Falludscha
Hoto: Reuters/A. Al-Marjani

"Muna rayuwa cikin fargaba dangane da abun da za mu sa a baki. Tsawon watanni uku ba mu da sukuni. Muna rayuwa ne a kan dabino da madara. Alhamdulillah tunda mun samu wannan. Mun kasa gudu saboda ba mu da kudi".

Sai dai a daidai lokacin da dakarun Iraki tare da goyon bayan na kasashen ketare ke kutsawa Falluja, sama da mutane 20 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren bama bamai da kungiyar ta IS ta yi ikirarin kaiwa. Munanan hare-haren na wannan safiya ta Litinin dai sun auku ne a unguwannin 'yan shi'a ta Shaab da ke yankin arewaci da Sadr da ke gabashin birnin na Bagadaza