Iraki za ta sasanta Saudiyya da Iran
August 13, 2017Talla
Al-Arjani ya ce yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed Bin Salman ne ya bukaci Iraki din ta shiga tsakani da nufin gyatta dangantakar da ta lalace tsakanin mahukuntan Tehran da na Riyadh. A shekarar da ta gabata ce Saudiyya ta yanke huldar jakadanci da Iran bayan da wani gungun mutane ya afkawa ofishin jakadancin Saudiyya da ke Tehran biyo bayan aiwatar da hukuncin kisan da Saudiyya ta yi wa wasu mutane 47 ciki kuwa har da wani fitaccen malamin Shi'a. A wancan lokacin dai Iran ta yi Allah wadai da afkawa ofishin jakadancin Saudiyya a kasarsarta har ma Shugaba Hassan Rouhani ya yi tayin biyan diyya amma kuma Saudiyya ta yi watsi da batun, lamarin da ya jefa kasashen cikin rikici na diflomasiyya.