Iran: An cafke masu hannu a harin juma'a da ta gabata
June 10, 2017Talla
Tun da farko ranar Jum'a da ta gabata humomin tsaro sun kame mutane 41 da ake tunanin suna da hannu a tagwayen hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 a majalisar dokokin kasar. Jami'an 'yan sanda na Iran din, sun kuma gano motar da maharan suka yi amfani da ita wajen kai hare-haren biyu na ranar Laraba a tsakiyar birnin kasar. Tuni dai Kungiyar IS ta dau alhakin kai wannan mummunan harin.