Iran ta kashe wasu masu yada kyamar Musulunci
May 8, 2023Talla
Iran ta kashe wasu mutane biyu da ta yanke wa hukuncin kisa a baya, bayan samunsu da laifin yin batanci ga addinin Musulunci. Kamfanin dillancin labaran kasar mai suna Mizan ne dai ya wallafa labarin a shafinsa na yanar gizo a wannan Litinin, amma ba tare da baiyana takaimaimen ranar da aka aiwatar da kisan ba.
Kamfanin ya nuna cewa, mutanen da aka aiwatar da kisan kansu, sun hada da Yousef Mehrdad da Sadrollah Fazeli Zare, sun kuma jima suna amfani da shafukansu na yanar gizo a wallafa ra'ayoyi na batanci da kuma yada kyamar addinin Islama, laifukan da suka saba wa dokokin kasar ta Iran.