Iran: An nada Ebrahim Raïssi a matsayin shugaban kasa
August 3, 2021Shi dai Raïssi da aka nada wanda kuma ya yi nasara a zaben watan Yuni, ya gaji Hassan Rohani mai matsakaicin ra'ayi wanda ya kulla yarjejeniya kan makamashin nukiliyar Iran tare da manyan kasashen duniya, bayan shekaru na sa-in-sa.
Sabon shugaban zai dukufa ne wajen yin aiki tukuru domin juya babin komabayan tattalin arzikin da takunkumin Amirka da annobar corona suka jefa Iran a cikin, Sannan zai koma kan teburin tattaunawa don ceton yarjejeniyar nukiliyar kasa da kasa da ke cikin mawuyacin hali. Sai dai tuni jagoran addini Khamenei ya bayana cewar za a dauki lokaci wajen warware matsalolin tattalin arziki da kasar ta Iran ke fuskanta.
A ranar Alhamis mai zuwa ne za a rantsar da Mista Raïssi a gaban Majalisar dokokin Iran, inda zai gabatar da sunayen wadanda yake son nadawa a mukaman minista.