Shugaban addini a Iran ya bayyana muhimmancin kada kuri'a
February 21, 2020Talla
Masana siyasa a kasar Iran na ganin cewa haramta wa wasu 'yan siyasa da yawansu ya kusan 9,000 masu akidun kawo canji shiga takarar kujerun zauren majalisar dokokin zai yi tasiri wajen fitar 'yan tsirarun mutane domin kada kuri'u a cibiyoyin zabe.
Zaben 'yan majalisar dokokin na gudana ne a lokacin da tattalin arzikin kasar Iran ke fuskantar kalubale sakamakon takunkumi da kuma wariyar da kasar ke fuskanta a bangaren diplomasiyya. Kusan 'yan takara dubu bakwai ne daga mazabu 208 suke neman zamowa wakilai a kujeru 290 na zauren majalisr dokokin kasar ta Iran.