1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kanada ta aiko da jami'ai Iran bayan hadarin jirgi

Gazali Abdou Tasawa
January 10, 2020

Hukumomin Iran sun sanar a wannan Juma'ar da cewa wani rukunin jami'an kasar Kanada na kan hanyar zuwa Iran domin kula da kayayyakin 'yan kasar ta Kanada da suka mutu a cikin hadarin jirgin sama.

https://p.dw.com/p/3Vzgk
Iran Flugzeugabsturz Ukraine International Airlines | Wrackteile bei Teheran
Hoto: AFP/Irna/A. Tavakoli

Hukumomin kasar Iran sun sanar a wannan Juma'a da cewa wani rukunin jami'an kasar Kanada guda 10, na kan hanyar zuwa kasar ta Iran domin kula da kayayyakin 'yan kasar ta Kanada da suka mutu a cikin hadarin jirgin saman nan na Boeing 737 na kasar Ukraine a ranar Larabar da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 176 akasarinsu 'yan kasar ta Kanada.

 Mahukuntan Landan da na Ottawa har ma da Amirka, na zargin wani makami mai lizzami na kasar ta Iran ne ya kakkabo a bisa kuskure jirgin na Ukraine Airlines International. Sai dai a sanarwar da ofishin ministan harakokin wajen kasar ta Iran ya fitar a wannan Juma'a, ya ce Teheran za ta gabatar wa duniya da sakamakon binciken dalilin faduwar jirgin.

 Kazali Iraki ta dauki alkawarin saka wakillan gwamnatin kasar ta Ukraine da na kamfanin jirgin da ma kwararru daga kasashen da hadarin ya rutsa da mutanensu a cikin aikin binciken da za ta gudanar.