1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da Saudiya sun amince da taimaka kawo karshen fadan darika a yankin

March 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuQf

Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmedinajad da sarki Abdalla na Saudiya sun amince suyi aiki tare domin kare yaduwar tashe tashen hankula na darika tsakanin musulmi a Iraqi da kuma sauran yankin gabas ta tsakiya.

A jiya asabar shugabanin biyu suka gana a lokacin wata yar gajeruwar ziyara da Ahmedinajad ya kai zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiya.

Jamian kanfanin dillancin labaru na kasar Saudiya sunce shugabanin biyu sun kuma jaddada muhimmancin hadin kann Palasdinawa da kuma bukatar dake akawai ta kare hadin kai da yancin kasar Iraq.

Kanfanin ya ruwaito Ahmedinajad na baiyana goyon bayansa ga kokarin saudiya na samarda zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Lebanon.