Iran da Saudiyya sun tattauna kan Hajji
March 5, 2017Talla
Iran ta ce an sami ci gaba mai ma'ana a tattaunawa da kasar Saudiyya domin barin 'yan kasar su gudanar da aikin hajjin bana duk da cewa akwai sauran batutuwa da ba'a kammala cimma matsaya a kansu ba.
A shekarar bara ce dai Saudiyya ta haramta wa 'yan Iran shiga kasar domin aikin hajji bayan da dangantakar diplomasiyya ta lalace tsakanin kasashen biyu da suka kuma suka kasa cimma daidaito kan matakan tsaro a lokacin aikin hajjin.
Kamfanin dillancin labaran Iran ya ruwaito wakilin jagoran addini na kasar Ali Ghazi yana cewa an warware galibin matsalolin da ke tsakanin kasashen, sai wasu 'yan kananan batutuwa kawai da suka rage.