Iran: Habakar tattalin arziki bayan dage takunkumi
Sukar da shugaba Trump na Amirka ya yi wa shirin nukiliyar Iran kamar kullum, yana hade da batun tattalin arziki. Tuni dai kamfanonin kasashen waje suka ci gaba da harkokin kasuwanci da kasar.
Sufurin jiragen saman Airbus
Kamfanin jiragen sama na IranAir ya yi odar jirage guda 100 kirar Airbus. Rukunin farko na jiragen sun isa a watan Janairu 2017.
Sufurin jirgin Boeing
Kamfanin Boeing da ke gogayya da Airbus shi ma ya sami oda daga IranAir na jirage 80.
Sufurin jiragen Airbus
Kamfanin Airbus shi ma ya sanya hannu a kan yarjejeniyar samar da jirage 45 ga kamfanin zirga-zirgar jiragen sama mai zaman kansa Iran Airtour da kuma jirage 28 ga kamfanin Zagros Airlines a yankin.
Jigilar jiragen Boeing
Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na uku mafi girma a Iran Aseman Airlines ya yi odar jiragen Boeing guda 30 a watan Yuni, hulda ta farko tsakanin Boeing da Iran tun bayan da shugaba Trump ya karbi shugabancin Amirka.
Der Zugverkehr: Siemens
A watan Oktoba 2016 kamfanin Siemens ya sanya hannu kan wata yarjejeniya domin sabunta hanyoyin jiragen kasa na Iran. Kamfanin na Munich da ke Jamus ya kuma samar da kawunan jiragen kasa wato Locomotive masu amfani da injin gas da na lantarki.
Jigilar jiragen kasa na kamfanin Alstom
Kamfanin Alstom wanda Siemens ke neman karbe ragamarsa ya sami kwantaragin aikin hadin gwiwa a Iran domin gina hanyar layin dogo na karkashin kasa ga jirage masu zirga-zirga na yanki.
Jiragen kasa na kamfanin CMC
Kamfanin CMC na China ya samar da jiragen kasa masu gudu da ke amfani da lantarki da ke zirga-zirga tsakanin Tehran da birnin Mashhad a arewa maso gabashin Iran.
Kamfanin Gazprom da OMV
Kamfanin mai na Ostiriya OMV da takwaransa na Rasha wato Gazprom Neft suna son gudanar da aikin hakar mai a kasar tare da hada hannu da kamfanin mai na Iran din NIOC.
Kamfanin mai na Wintershall
Ko da yake BASF reshen kamfanin Wintershall ya sanya hannu a kan takardar kudirin aiki da kamfanin mai na NIOC na Iran a watan Aprilu 2016, sai dai shugaban kamfanin BASF Kurt Bock a watan Fabrairun 2017 ya ce ba a yanke shawarar zuba jari ba tukunna.
Kamfanin mai na Shell
Kamfanin mai na Birtaniya Shell, a watan Disamba 2016 ya rattaba hannu a kan kwarya-kwaryar yarjejeniya ta bunkasa ayyukan mai da makamashin gas na Iran a kudancin Azadegan da Yadavaran da kuma Kish.
Kamfanin mai na Total
Kamfanin mai na Faransa, Total a watan Nuwamba 2016, ya zama kamfanin mai na farko na yammacin Turai da ya sami kwangila daga Iran bayan da aka dage mata takunkumi. Gagarumin aiki a babbar tashar makamashin gas mafi girma a duniya, a kudancin Pars.
Kamfanin motoci na VW
Kamfanin Volkswagen ya sake komawa Iran bayan shekaru 17 kuma cikin kankanin lokaci ya tura motocinsa samfurin Tiguan da Passat.
kamfanin motoci na Daimler
Kamfanin Daimler ya samar da manyan motoci samfurin Fuso ta hanyar kamfanin Khodro da Iran.
Kamfanin motoci na Renault
Kamfanin Renault ya sami kwantaragin hadin gwiwa a Iran inda za su rika kera motoci dubu 150 a kowace shekara.
Kamfanin motoci na Peugeot
Kamfanin Peugeot kafin a sanya wa Iran takunkumi shi ne kamfanin motoci na Turai mafi girma a kasar. Tun daga 2016 ya sami kwangiloli da dama na kera motoci da ma samar da sabon samfuri tare da hadin gwiwa da kamfanonin Iran.
Hada-hadar kudade da babban Banki
Babban bankin Ostiriya ya kasance banki na farko a tarayyar Turai da a watan Satumba ya sanya hannu domin kulla harkokin kasuwanci da Iran bayan cire mata takunkumi.