1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty International ta ce tana da shaidun kisan

Abdourahamane Hassane
March 4, 2020

Wani rahoton da kungiyar kare hakin dan Adam ta kasa da kasa Amnesty international ta bayyana ya nuna cewar akalla yara 23 jami'an taro suka kashe a Iran a lokacin wata zanga-zangar a bara.

https://p.dw.com/p/3YppX
Iran Unruhen in Teheran
Hoto: Mehrnews

Kungiyar ta ce yara 'yan shekaru 12 zuwa 17 jami'an tsaron suka bindige har lahira a ciki har da yarinya 'yar shekaru takwas zuwa 12. Amnesty Internationa ta ce ta bayyana rahoton ne bayan binciken da ta gudanar, wanda ta ce ta tattara hotuna da bidiyo na shaidu. A cikin watan Nuwambar bara ne zanga-zanga ta barke a kasar ta Iran bayan da gwamnati ta kara frashin man fetir.