1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: mun karbi samfurin makaman nukiliya

Kamaluddeen SaniApril 11, 2016

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewar Rasha ta aike wa kasar da rukunin farko na makamai masu linzami masu cin dogon zango.

https://p.dw.com/p/1ITJc
Iran Reaktor Bushehr
Hoto: Getty Images/IIPA

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran Jaber Ansari ya ce tuni samfarin tsara makaman suka isa kasar, bayan cimma matsaya da mahukuntan Rasha, a inda yarjejeniyar ta lakume sama da Dala miliyan 900.

Ratotannin da ke fitowa daga Iran suka ce tun a watan Fabirerun wannan shekarar ta 2016 mahukuntan birnin Moskow suka so aiko da yadda tsarin makaman linzamin suke samfurin S-300 zuwa Iran a yayin da hakan ya ci tura sai yanzu.

Tun dai a shekara ta 2007 kasashen Rasha da Iran suka sanya hannu a kan yarjejeniyar samar da tsarin makaman masu linzami. Amma Rasha ta tsahirta saboda da takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wa Iran a kan batun makaman.