1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty Internanational ta zargi hukumom Iran

Abdourahamane Hassane
June 29, 2022

Kungiyar kare hakkin bil' Adama ta Amnesty International ta zargi hukumomin Iran da azabatar da mai fafutukar kare hakkin bil' Adaman nan Narges Mohammadi ta hanyar hana mata magunguna masu mahimmanci ga lafiyarta.

https://p.dw.com/p/4DROK
Narges Mohammadi
Narges Mohammadi Hoto: Hrana

Mijin Narges mazaunin birnin Paris,Taghi Rahmani, ya zargi hukumar gidan kurkukun mata na Qarchak da ke kusa da Tehran a kan shafukan sada zumunta da kwace maganin huhu da danginta suka aika mata. Narges, mai shekaru 50, wacce ke fama da cututtukan huhu da zuciya, an kwantar da ita a asibiti sakamakon bayyanar rashin numfashi da kuma ciwon zuciya, amma tun bayan da ta koma gidan yari an hanata samun wasu magungunan da take bukata a cewar Amnesty International. A halin yanzu, Narges Mohammadi tana zaman gidan yari na shekaru goma da watanni takwas a wasu kararraki guda biyu, ciki har da hukuncin daurin rai da rai a kan yada farfaganda nuna kiyaya ga gwamnatin Kasar Iran.