1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na ci gaba da kamun kafa na diflomasiyya

Salissou Boukari
May 15, 2018

Shugaban diflomasiyyar kasar Iran Mohammad Javad Zarif na ci gaba da rangadin kasashen masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar nukiliyar kasar a wani mataki na neman kare yarjejeniyar bayan fitar Amirka.

https://p.dw.com/p/2xkuz
Österreich Atomverhandlungen mit dem Iran in Wien
Shugaban diflomasiyyar kasar Iran Mohammad Javad Sarif da Federica MogheriniHoto: Reuters/L. Foeger

Bayan ya ziyarci kasashen China da Rasha, a wannan Talatar ce shugaban diflomasiyyar na Iran zarif ya isa a birnin Brussels, inda ya gana da shugabar diflomasiyyar Tarayyar Turai Federica Mogherini, kafin da yammaci kuma ya gana da takwarorinsa na Jamus da Faransa da Britaniya.

Babbar ayar tambayar dai a nan ita ce, ta yaya za a iya tafiyar da wannan yarjejeniyar bayan ficewar Amirka, da kuma yadda za a kare muradun kasar Iran da suka shafi harkokin tattalin arziki ta hanyar yarjejeniyar kamar yadda wata majiya ta diflomasiyyar kasashen Turai ta sanar.

Ana sa ran dai shugabannin na Tarayyar Turai za su fitar da wata matsaya guda kan wannan batu yayin wani babban taro da za su yi a ranar Alhamis mai zuwa a birnin Sofiya na kasar Bulgeriya.