Iran na iya tada yaƙin cacar baka - inji William Hague
February 18, 2012Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague yace babu ko tantama Iran na ƙoƙarin ƙera makamin ƙare dangi. A hira da ya yi da wata mujalla da aka wallafa a ranar Asabar, William Hague yace wannan wani babban bala'i ne ga al'amuran duniya wanda kuma ka iya haifar da sabon yaƙin cacar baka a yankin Gabas Ta Tsakiya.
A waje guda kuma kantomar harkokin wajen ƙungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton tare da sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton sun yi lale marhabun da ƙudirin da Iran ta nuna na komawa kan teburin tattaunawa a game da shirinta na nukiliya. Cikin taka tsantsan Ashton ta ce ta yi imani Tehran za ta dawo kan teburin shawarwari. "Ina so na baiyana cewa ina tsammanin abu ne mai kyau da muka sami wasiƙa daga Iran game da komawa kan teburin tattaunawa, a saboda haka muna gani akwai alamun ƙwaƙƙwarar ƙudiri cewa mai yiwuwa Iran a shirye take ta koma tattaunawa. Za mu cigaba da shawartawa domin tabbatar da cewa saƙon da muka samu sahihi ne."
Ita ma dai a na ta ɓangaren sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta buƙaci Iran ta zo da masalaha domin kawo ƙarshen taƙaddama kan shirin nukiliyar. Mashawarcin Iran kan shirin nukiliya Saeed Jalili a cikin wata wasika da ya aikewa Catherine Ashton ya yi tayin komawa tattaunawar ba tare da jinkiri ba. Ƙasashen yammacin turai dai na zargin Iran da fakewa domin ƙera makamin ƙare dangi.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu