1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran na kyamar rigakafin coronar kasashen yamma

January 11, 2021

Majalisar dokokin Iran ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta haramta amfani da rigakafin corona da aka sarrafa a kasashen yamma. Sai dai gwamnatin Shugaban Iran Hassan Rohani ta nesanta kanta da irin wadannan kiraye-kiraye

https://p.dw.com/p/3nmfw
Iran  Mohamad Bagher Ghalibaf  Parlamentspräsident
Hoto: Getty Images/AFP

Matsayar ta majalisar na kara jadadda shakkun da jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya nuna a game da rigakafin a makon da ya gabata. 'Yan majalisar sun ce tun da har aka fara samun labarin rigakafin da kasashen yamma suka sarrafa ta haifar da rashin lafiya da kuma mutuwa a wasu wuraren to bai dace Iran ta yi amfani da ita ba.

Gwamnatin Shugaban Iran Hassan Rohani ta nesanta kanta da irin wadannan kiraye-kiraye, sai dai ita ma ta nuna damuwa kan sahihancin rigakafin. Duk wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar lafiya ta duniya, WHO, da wasu kasashe suka yi bincike kan rigakafin ba tare da sun gano tana da illa ga lafiyar dan Adam ba.