Iran na son a kyale ta ta tafiyar da aikin samar da Uranium da kanta
November 12, 2005Gwamnatin Iran ta dage kan matsayin ta a game da samar da karafan uranium da kanta. An jiyo haka ne daga bakin mai kula da shirin nukiliyar Iran Ali Larijani bayan shawarwarin da suka yi da ministan harkokin wajen Rasha kuma shugaban majalisar tsaron kasa Igor Ivanov a birnin Teheran. Larijani ya ce muhimmin abu a gare su shi ne a kyale su su tafiyar da fasahar nukiliya, amma duk da haka gwamnati na maraba da ko-wace irin shawara da za´a bayar da nufin warware takaddamar da ake yi dangane da shirin ta na nukiliya. Da farko dai Rasha ta ba da shawarar samarwa Iran din karafan Uranium, shawarar da KTT ke goyawa baya. Shi kuwa a nasa bangaren Ivanov ya ce shi kam aikin sa shi ne ya taimaka a farfado da shawarwarin da ake yi tsakanin Iran da kuma wakilan tarayyar Turai.