1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro kan shirin nukiliyar Iran a birnin Vienna

Abdul-raheem Hassan MNA
September 1, 2020

Jami'an gwammnatin Iran da hukumomin kula da yarjejeniyar nukiliyar 2015 na yin taro a birnin Vienna domin kare yarjejeniyar daga rushewa.

https://p.dw.com/p/3hq1b
Iran Isfahan Kernkraftwerk
Hoto: Getty Images/AFP/H. Fahimi

Ganawar a birnin Vienna na kasar Ostiriya na zuwa ne a daidai lokacin da Amirka ke kara matsin lamba kan tsaurarawa Iran takunkumi.

Kasashen Birataniya da Faransa da Jamus hada da China da Rasha na kokarin ganin sun shawo kan Iran ta mutunta yarjejeniyar bayan sanar da ci gaba da habaka ayyukan nukiliyarta a shekarar 2019 bayan ficewar Amirka daga yarjejeniyar a 2018.

A makon da ya gabata hukumomin kula da makamashi a Iran sun amince wa jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido kan nukiliya su ziyarci cibiyoyin gudanar da ayyukan nukiliyar a kasar.