Iran na yunkurin kawo karshen yakin Yemen
March 12, 2023Talla
A cikin sanarwar da wakilicin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya yi nuni da cewa farfado da dangantaka tsakanin gwamnatin Teheran da Riyadh zai bayar da damar sake sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta da ma zama kan teburin tattaunawa don dinke barakar da ke damun gwamnatin hadin kai a Yemen.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ce, kasashen biyu suka amince da sake farfado da huldar diflomasiya a tsakaninsu tare da bude ofisoshin jakadancinsu bayan shafe tsawon shekaru 7 suna zaman doya da manja. Tun bayan rashin fara ga maciji da juna a shekarar 2014 ne dai gwamnatin Saudiyya ke jagorantar kawancen soja na gwamnatin Yemen yayin 'yan tawayen Houthi da ke yaki da gwamnati ke samun goyon bayan Iran.