1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran Attentat

January 12, 2012

Kisan gillan da aka yi wa ɗaya daga cikin ƙwararrun masana kimiyyar nukiliyar Iran, ya sake zurfafa lalatacciyar dangantaka dake tsakanin Iran da Izraela

https://p.dw.com/p/13iBb
Seit 2011 sind im Iran durch gezielte Attentate vier iranische Atomwissenschaftler ermordet worden. Hier wird Majid Shahriari zum Grab getragen. Quelle: IRNA Lizenz: Frei
Hoto: IRNA

Gidan talabijin din Iran din dai ta nunar da hoton inda wannan kisan gilla ya auku. Sauran abunda ya rage daga burbuɗin tarwatsattsiyar motar a wani babban titin cunkoson jama'a  ayanin arewa maso gabashin Tehran. Gefen motar kuwa ana iya ganin jini kota ina, a yayin da ɗaruruwan jama'a suka yi dafifi domin gane wa idanuwansu wannan hari na bomb.

Waɗanda suka gane wa idanunsu dai sun shaidar da cewar, wasu mutane biyu dake kan Babura ne suka ɗana bomb din a motar masanin kimiyyar nukiliyar kasar ta Iran da mayen ƙarfe. Jim kadan da ɗawawarsa ne bomb din ya tarwatse , nan take Mostafa Ahmadi Roshan mai shekaru 32 da haihuwa ya riga mu gidan gaskiya. Ayayinda wasu mutane biyu suka samu raunuka.

Seit 2011 sind im Iran durch gezielte Attentate vier iranische Atomwissenschaftler ermordet worden. Hier eine Bombe zerfetzte das Auto des Wissenschaftlers. Quelle: IRNA
Hoto: IRNA

Kafin mutuwarsa dai kwarraren masanin kimiyyar Nukiliyar ya kasance mataimakin directa a tashar inganta sinadran Uranium na kasar dake birnin Natanz. Wannan cibiyar tana inganta sinadran uranium da zai samar samar da makamashin nukiliya, wanda kuma za'a iya amfani da shi wajen kera makamai na nukiliya.

Wannan harin dai ya kasance daidai da wasu guda hudu da suka auku a shekaru biyun da suka gabata a kasar ta Iran. A waɗannan hare haren dai kwararru ta fannin kimiyya guda uku, biyu daga cikinsu wadanda ke aiki a shirin nukiliyyar Iran mai kaddama sun rasa rayukansu, ayayinda guda wanda a yanzu ke jagorantar hukumar makamashin Aton na kasar ya tsira da ransa. Babu abunda kafofin yada labaran Iran din ke nunar wa ko magana akai a yau, face harin na jiya laraba daya kashe Mostafa Ahmadi Roshan.

Kwararru kan lamura daka je su zo dai sun soki kasashen yammaci na turai, dangane da yadda suka yi biris kan wannan kisan gillan masanin kimiyya na Iran, batu da wasu kafofin yaɗa labaru ke kira da aramawa kura aniyarta kan Izraela.

In this photo provided by the semi-official Fars News Agency, people gather around a car as it is removed by a mobile crane in Tehran, Iran, Wednesday, Jan. 11, 2012. Two assailants on a motorcycle attached magnetic bombs to the car of an Iranian university professor working at a key nuclear facility, killing him and wounding two people on Wednesday, a semiofficial news agency reported. (Foto:Fars News Agency, Mehdi Marizad/AP/dapd)
Hoto: AP

Tun a jiya laraba nedai mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Reza Rahimi, da ma'aikatar harkokin waje da majalisar dokokin Iran dama wasu manyan jami'an kasar suka ɗora alhakin harin bomb na jiyan akan Izraela da uwar ɗakinta Amurka.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka hillary Clinton ta wanke Amurka da cewar, bata da hannu a kisan da akayi wa Mostafa Ahmadi Roshan.

Kafofin yada labarun Izraela a nasu ɓangaren sun yi bitar labarun dake nunar da hafsan sojin kasar Lieutenant general Benny Ganzt ke cewar, shekara ta 2012 zata kasance mawuyaci wa Iran.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita          : Umaru Aliyu