1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na ƙoƙarin shawo kan ƙasashen duniya game da rikicinta

November 7, 2012

Ƙasashen duniya na bukatar samar da wani yanayi na kawar da makaman nukiliya a duniya baki ɗaya.

https://p.dw.com/p/16e12
Hoto: yjc.ir

A nan gaba a cikin watan Disamba ne za a shirya wani babban taro a kan batun makaman nukiliya a cikin yankin Gabas ta Tsakiya wanda ƙasar Finland za ta karɓi baƙoncinsa, taron da kuma ƙasar Iran ta ce za ta halarta domin nuna bukatar duniya da a yi watsi da batun makaman nukiliya.
Jakadan ƙasar ta Iran a hukumar kasa da ƙasa ta makamashi Ali Asghar Soltanieh ya faɗi hakan ne a yayin wata hira da ya yi da manema labarai, inda ya ce ƙasarsa za ta gwada wa duniya cewa shirinta na neman makamashin farar fula ne kawai. To sai dai yanzu haka ƙasashen duniya na ganin ƙasar ta Iran na shirye shiryenta na ƙarshe a matakin samar da makaman nukiliya nan da shekara ta 2013. Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ƙara jaddada cewar kasarsa a shirye ta ke ta aukawa Iran domin wargaza wannan shirin na makaman nukiliya.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Mohammad Nasiru Awal