Yarjejeniyar nukiliya na tangal-tangal
May 8, 2019Wannan mataki na Iran dai na zuwa ne, shekara guda bayan da Amirka ta ce ta janye daga yarjejeniyar da aka kulla da Iran a shekarar 2015. Shugaba Hassan Rowhani ne dai ya gabatar da wannan shiri na Iran ga kasashen Jamus da Chaina da Faransa da Birtaniya da Rasha a wani sako da ya aike musu. A cewar ministan harkokin wajen Iran din, Mohammad Javad Zarif Amirka ita ce kanwa uwar gami na dalilin da ya sa kasar ta dau wannan mataki, inda ya ce gwamnatin Amirkan ba ta mutunta doka.
Ita ma da take mayar da nata martanin Rasha ta bakin ministan harkokin wajenta Sergei Lavrov cewa ta yi komwar da Iran ke kokarin yi wajen mallakar makamin nukiliya ya faru ne saboda matakin Amirka. Wata kasar da ke da muhimmanci a yarjejeniyar na zama Chaina, kuma a cewar Geng Shuang da ke magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Chainan, su dama sun samar da yanayi da Iran za ta iya aiwatar da sharuddan da aka sanya mata karkashin yarjejeniyar, amma takunkumin Amirka ya kawo masu cikas.
Iran ta gaji ta jiran gawon shanu
Iran dai ta nunar da cewa ta dauki tsawon shekara tana jiran ganin abin da kasashe da ke cikin yarjejeniyar za su yi mata, da zai rage mata radadin takunkumin na Amirka domin ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar kafin daukar wannan mataki. Sai dai a nata bangaren Jamus kamar takwararta wato Faransa ta nuna rashin jin dadinta ga matakin da Iran din ta dauka, ta ce tana tuntubar dukkanin kassahen da suka yi saura a yarjejeniyar da aka kulla a 2015. Har ila yau ta kuma nunar da bukatar ganin Iran ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar kamar yadda Heiko Maas ministan harkokin wajenta ya nunar.
Shugaba Rowhani dai ya ce kasar za ta ci gaba da shirin karfafa ayyukanta da suka shafi sinadaran Uranium, hakanan sun ba da kwanaki 60 na sababbin sharudda kan yarjejeniyar ta nukiliya. Idan babu sharudda masu kyau, nan da lokacin za su ci gaba da abin da suka sanya a gaba. Sai dai Mike Pompeo ya ce suna zura ido suga abin da Iran din za ta yi. A shekara ta 2015 ne dai aka cimma yarjejeniyar da Iran, inda aka bukaci ta takaita shirinta na makamashin na nukiliya, sai dai Amirka na zagon kasa ga mafarkin kasashen da ke da buri na dasawa da kasar ta Iran mai albarkatun mai.