1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Rohani na Iran ya yi kakkausar suka ga Amirka

Abdoulaye Mamane Amadou
September 22, 2019

Kasar Iran ta soki lamirin jibge jami'an tsaro a yankin tekun fasha, tare da bayyana anniyarta ta gabatar da wata taswirar tattabatar da tsaron yankin ga Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/3Q312
Iran Militärparade in Teheran | Präsident Hassan Rohani
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Iranian Presidency Office

A yayin da yake jawabi a wani bukin faretin soja a birnin Téhéran, Shugaba Rohani ya ce yankin na tekun fasha na cikin wani yanayi mai cike da tarihi, kan daga bisani ya soki duk wani batun jibge bataliyoyin soja daga wasu kasashen ketare a yankin, yana mai cewa hakan ka iya kara dagula al'amurran tsaro da zaman lafiyar yankin.

Jawabin shugaban na zuwa ne kwanaki bayan matakin da kasar Amirka ta dauka na kara jibge adadin sojojinta yankin tekun fasha a wani mataki na tauna tsakuwa kan kasar Iran, wacce Amirka da Saudiyya ke zarginta da alhakin kai hari a wasu matatun man fetir din kasar Saudiyya a makon jiya.