Amirka ta laftawa Iran takunkumai
June 24, 2019Talla
Shugaban Amirka Donald Trump ya sanya hannu kan sababbin takunkuman na karya tattalin arziki ga Iran. Trump ya ce za su ci gaba da matsawa Tehran kaimi duk da taka tsan-tsan da suke yi na kaucewa afkuwar yaki da ita, sai dai ba wai hakan na nufin za a bar Iran din ta ci gaba da bunkasa makamashinta na nukiliya ba.
A wannan karon dai Trump ya ce takunkuman za su shafi ofishin jagoran juyyin-juya halin Musulunci na Iran din Ayatollah Ali Khamenei. Iran dai ta dogara ne kan albarkatun man da take fitarwa, ana kuma ganin matakin ka iya kara jefa tattalin arzikinta cikin mawuyacin hali.