Iran: Shugaba Rouhani ya yi tir da wani aikin majalisa
December 2, 2020Talla
Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran ya bayyana adawarsa da wani kudurin dokar da majalisar kasar ta amince da shi, inda zai dakatar da sa idon Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin makamashin Uranium na kasar.
Ra'ayin shugaban na Iran ne cewa matakin majalisar dokokin kasar zai maida hannun agogo baya a kokarin da ake yi na dawo da yarjejeniyar Nukiliyar kasar da aka cimma a 2015.
Jayayya kan kudurin dokar wanda ya samo karfi bayan kisan wani gwanin kimiyyar Nukiliyar makon jiya a kasar na tabbatar da karfin adawa da ke tsakanin Shugaba Rouhani mai matsakaicin ra'ayi da kuma 'yan majalisar kasar mai tsaurin ra'ayi.
Iran din dai na kokari a yanzu na ganin yadda za a kwance mata takunkuman tattalin arziki da Amirka ta kakaba mata.