Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutum uku
May 19, 2023Talla
Shafin Intanet na kotun Mizan da ke Iran din, ya sanar da aiwatar da hukuncin kisan ne a kan Majid Kazemi da Saleh Mirhashemi da kuma Saeed Yaghoubi da jijjifin safiyar wannan Juma'ar.
Hukumomin na Iran dai sun ce mutanen uku sun kashe wasu jami'an 'yan sanda biyu a cikin watan Nuwamba lokacin gangamin nuna kyama ga gwamnatin a shekarar da ta gabata.
Kungiyoyin kare hakkin bil Adama wadanda da ma suka yi ta yi tir da wannan hukuncin, sun ce an azabtar da mutanen uku da aka kashe a yau tare da tilasta musu amsa laifi a kafofin talabijin, sannan kuma ba a bi shari'ar yadda ya kamata ba.