Iran Uran Türkei
May 17, 2010Ƙasar Iran ta ba da kai bori ya hau game da shirinta na nukiliya saboda cewa a yanzu ta amince a bunƙasa uranium ɗinta a wata ƙasa daban. A yau ne aka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya tare da ƙasashen Turkiyya da Brazil, kuma ana ganin hakan a matsayin dama ta ƙarshe da Iran ke da ita wajen kauce wa fuskantar ƙarin takunkumi.
An gano wannan mataki na Iran tamkar mataki na ba-zata da aka ɗauka sakamakon tattaunawar da ta gudana. Za a iya cewa a ƙarshe, Shugaban Brazil, Lula da Silva, da fraministan Turkiyya, Reccep Tayyep Erdogan sun iya su shawo kan gwamnatin Iran bayan da aka shafe watanni ana ta kace-kace-na-ce game da tayin da aka mata cewa ta bari a bunƙasa mata uranium ɗinta a watan ƙasa daban. Yarjejeniyar wadda aka rattaba hannu akanta da safiyar yau Litinin a birnin Tehran, ta buƙaci jamhuriyar ta Islama ta yi jigilar ton guda da ɗigo biyu da ke zaman kashi uku da ɗigo biyar daga cikin ɗari na sinadirin uranimun da take mallaka zuwa ƙasar Turkiya. Daga nan ne kuma, a ƙarƙashin kulawar hukumar makamashi ta ƙasa da ƙasa wato IAEA za a yi mata musayar kashi 20 daga cikin ɗari na uranium ɗin da take buƙata sabo da bincike na aikin magani, daga ƙasashen Rasha da Faransa.Tun lokacin hunturun bara ne dai aka yi wa Iran wannan tayi. Amma sai gwamnatin Iran ta ce wajibi ne a aiwatar da wannan shiri a cikin ƙasar. Lula da Erdogan sun nuna matuƙar gamusuwarsu da cimma wannan daideto . Akan haka babban mashawarcin Iran kan shirinta na nukiliya, Ali Akbar Salehi ke cewa: "Mun amince da wannan shiri ne bisa dagewar da ƙasashen yamma suka yi cewa a yi jigilar ɗanyen Uranium ɗinmu zuwa wata ƙasa daban ba don komai face don bayyanar da fatan na alheri da kuma kudurinmu na yin haɗin-gwaiwa.Tun da farko sai da Erdogan ya soke ziyarar da ya yi shirin kaiwa birnin Tehran domin nuna fushinsa game da matsayin Iran na ƙin amince da wannan shiri. Saboda cewa Turkiya ta yi amfani da hanyoyi da dama wajen shiga tsakani. Amma nan take fraministan na na Turkiya ya tashi zuwa babban birnin na Iran sakamakon kyakyawar alama da aka samu daga tattaunawar da ta gudana tsakanin Lula da gwamnatin Iran, kamar yadda wani shahararren masanin siyasa a Turkiya, Mustafa Kibaroglu ya nunar: "Za a iya cewa ƙasar Turkiya ta samu nasara wajen bin hanyar diplomasiya da ta samar da wannan tattaunawar. Kuma a haƙiƙa wannan abun azo a gani ne, ko da yake hakan bai nufin kau da dukkan rikice-rikice da ke tsakanin ƙasashen yamma da ƙasar Iran."
Gaskiyar lamarin dai shi ne a yanzu an kau da taƙaddamar da ake yi game da shirin nukiliyar Iran. Amma kuma za a ci gaba da saka ayar tambaya game da ko ƙasar Iran za ta yi amfani ne da shirinta na nukiliya ne saboda dalilai na aikin soja.
Mwallafi: Ulrich Pick/ Halima Abbas
Edita: Halima Abbas