1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Amirka na neman yamutsa Turai

Yusuf Bala Nayaya
February 17, 2019

Ministan harkokin wajen Iran ya ce bukatar mataimakin shugaban Amirka ta ganin kasashen Turai sun fita daga cikin yarjejeniyar nukiliya da suka kulla a shekarar 2015, jawo rikici ne a Turai.

https://p.dw.com/p/3DXSD
Deutschland München MSC Mohammed Dschawad Sarif
Hoto: AFP/C. Stache

Ministan harkokin wajen Iran ya yi kalamai masu zafi kan mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence inda ya ce zargin da Pence ya yi wa Iran kan cewa tana da tsari na "nuna kyama", kalamai ne na "tsana" da "rashin sanin yakamata". Mohammad Javad Zarif ya bayyana haka ne a lokacin taron kolin tsaro a duniya na birnin Munich a Jamus. Zarif ya kara da cewa bukatar Pence ta ganin kasashen Turai sun bi sahun Amirka wajen fita daga cikin yarjejeniyar nukiliya da suka kulla a shekarar 2015, wannan ba wani abu ba ne face kira na samar da tabarbarewar tsaro a tsakanin kasashen na Turai.

Har ila yau Zarif ya kara jan hankali ga mahukunta a Brussels da su kara azama a shirin da suke yi na tallafar kasuwanci da Iran muddin suna so yarjejeniyar da suka kulla a baya ta dore.