Iran ta ce a shirye take ta tattauna da Italiya kan batutuwan da suka shafi yanki Gabas Ta Tsakiya.
November 17, 2006Ofishin Firamiyan Italiya, Romano Prodi, ya tabbatad da samun wata wasiƙa ta musamman daga shugaba Mahmoud Ahmadinijad na ƙasar Iran, inda ya bayyana shirinsa na tattaunawa da Italiyan a kan batutuwan da suka shafi yankin Gabas Ta Tsakiya. Takardar, wadda wani jami’in diplomasiyyan Iran ya miƙa ta hannu da hannu ga ofishin Firamiyan da ke birnin Rom, ta iso ne kwana ɗaya bayan da Faransa da Spain da Italiyan suka gabatar da wani shiri na samad da zaman lafiya a yankin na Gabas Ta Tsakiya, inda suka nanata muhimmancin rawar da nahiyar Turai za ta iya takawa, wajen kawo ƙarshen zub da jinin da aka shafe shekaru aru-aru ana yi tsakanin Isra’ila da al’umman Falasɗinu.
A tattaunawar da suka yi da mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Jalili, yau a birnin Rom, Firamiya Roman Prodi da ministan harkokin wajen Italiyan Massimo D’Alema sun yi marhabin da sha’awar da Iran ta nuna, ta shiga cikin shawarwarin zaman lafiyar na Gabas Ta Tsakiya. Sai dai Italiyawan sun kuma yi kira ga Iran da ta bi hanya ta gari da kuma yin amfani da angizonta, wajen samo kwanciyar hankali a yankin.