Iran ta yi fatali da shirin kayyade yawan fetir
February 17, 2016Kasar Iran ta yi watsi da shawarar da wasu manyan kasashe hudu masu arzikin man fetir suka amince da ita game da shirin kayyade yawan mai da suke hakowa. Wakilin kasar a kungiyar kasashe masu arzikin man fetir ta OPEC, Mehdi Asali ya ce kasarsa ba za ta shiga cikin wannan shiri ba, yana mai cewa hasali ma kasarsa za ta kara yawan man da take hakowa ne har sai ta kai adadin da take samarwa gabanin sanya mata takunkuman karya tattalin arziki. Shi ma ministan albarkatun mai na kasar Bijan Namdar Zanganeh ya ce ba za su shiga cikin wannan shiri ba.
"Sun tattauna kan rage yawan man da ake hakowa. Muna da ja kan wannan batu, muna kuma neman karin bayani, shi ya sa dole su zo su tattauna da mu. Mun san mai yayi yawa a kasuwannin duniya amma Iran ba za ta rage kason da take samarwa ba."
A wannan Laraba dai ministocin mai na Venezuela da Iraqi za su je birnin Teheran don tattaunawa da takwaransu na Iran a kan batun, bayan da a ranar Talata ministocin mai na kasashen Rasha da Saudiyya da Qatar da kuma Venezuela suka amince da kayyade yawan mai ya zuwa matsayinsa na watan Janeru.