1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ce babu mai tauye mata `yancinta

November 22, 2007
https://p.dw.com/p/CQId

Babban mai shiga tsakani na Iran a kan rikicin nukiliyarta Saeed Jalili ya ce zai tattauna tsakaninsa da sakatare mai kula da manufofin waje na Kungiyar Taraiyar Turai Javier Solana a ranar 30 ga watan Nuwamba kan aiyukan nukiliya na ƙasar wanda ƙasashen yammacin duniya suke tsoron makaman nukiliya take ƙoƙarin ƙerawa.ya ce shekaru biyu ke nan Iran ta dakatar da inganta Uraniyum,hakazalika ba zata amince a tauye mata hakkinta ba.Jalili yana magana ne da manema labarai kafin wani babban taro da suka kira kan rahoton shugaban hukumar kare yaɗuwar nukiliya .A halin da a ke ciki dai yanzu a yau ne ake sa ran Muhamad El Baradei zai nemi goyon baya daga hukumar gudanarwa ta IAEA kan rahoton da ya miƙa wanda ya ke nuna cewa ta bada haɗin kai wajen amsa dukkan tambayoyi da a ak yi mata game da shirinta na nukiliya.

Sai dai kuma jamian diplomasiya kansu ya rarrabu game da ko amsa tambayoyin da Iran din ta yi ya isa a ɗage batun sake laƙaba mata takunkumi.