1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ce cinikin mai ba fashi

April 30, 2019

Kasar Iran ta ce ko a jikinta, dangane da barazanar da Amirka ta yi na haramta wa kasashe sayen danyen manta. Kasar ta ce cikin 'yan watannin da ke tafe za ta fara fitar da man.

https://p.dw.com/p/3Hg9y
Iran Hassan Rohani
Hoto: Reuters/S. Chirikov

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, ya ce kasarsa za ta ci gaba da fitar da danyen manta zuwa kasashen duniya, duk da barazanar da Amirka ke yi na kakaba mata takunkumai.

Shugaba Rouhani ya fadi haka ne a jawabin da ya yi wa al'umar kasar a ranar Talata, wanda aka watsa kai tsaye ta kafofin watsa labarai.

Ya ce kuskure ne Amirka ke yi na cewar Iran ba ta isa ta fitar makamashinta zuwa wasu kasashen ba, matakin da ya lashi takobin ganin bayansa.

A cewarsa nan da 'yan watanni, Amirka za ta soma ganin yanda Iran za ta fitar da albarkatun nata na mai, zuwa kasashen da Amirkar ba ta yi zato ba.