Iran ta ce ta yi nasarar gwajin makamai
February 10, 2014Iran ta ce ta yi nasarar gudanar da gwajin makamai masu linzami biyu a jajibirin bukin cika shekaru 35 da gudanar da juyin juya halin Islama.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar na IRNA ya rawaito ministan tsaron ƙasar Hossein Dehgan yana bayyana cewa sun gwada makaman ba tare da wani tangarɗa ba .
Shirin makamai masu linzamin na Iran ya daɗe yana sanya ƙasashen yamma cikin damuwa inda suke ganin ana iya amfani da shi wajen kai hari kan Israila.
Shugaban ƙasa Hassan Rohani wanda ya yi alƙawarin haɗa kai da ƙasashen yamma ta fiskar diplomasiyya ya taya al'ummar Iran da shugaban addini Ayatollah Ali Khamenei murnar nasarar gwajin makaman, ya kuma ƙara jaddada cewa da gaske yake dangane da shiga yarjejeniya da manyan ƙasashen duniya kan shirin makamashin nukiliyar ƙasarmai tattare da sarƙaƙiya.
Da daɗewa ne Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da Amirka da ƙungiyar Tarayyar Turai suka sanya mata takunkumi dangane da waɗannan makamai.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh