Iran ta ce 'yan kasarta ne maharan Tehran
June 8, 2017Talla
Mahukuntan kasar Iran sun ce maharan da suka afka wa kasar a wannan Laraba, wasu 'yan kasar ne da ke cikin kungiyar IS da ke gwagwarmaya a kasashen Iraki da kuma Syria. Ma'aikatar leken asirin kasar ta ce biyar daga cikin maharan wadanda aka kashe su lokacin da suka kai harin, mutane ne da suka hakkake su a matsayin mayakan jihadi na IS.
Rundunar mayakan kundumbalan kasar ta zargi kasar Saudiyya da hannu cikin lamarin, a kokari na ta'azzara lamura tsakanin Sunni da kuma bangaren Shi'a da ke Iran din. A ranar Laraba dai kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a majalisar dokokin Iran da kuma hubbaren Ayatollah Khomeini inda mutane 17 suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata.