1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ce za ta yi nazarin sabon tayin da aka gabatar mata a kan batun makamashin nukiliyanta.

June 7, 2006
https://p.dw.com/p/Buv5

Ƙasar Jumhuriyar Islama ta Iran, ta ce za ta yi nazari a hankali, kan sabon tayin da zaunannun ƙasashe na kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Jamus, suka gabatar mata, a wani yunƙurin da suke yi na shawo kan mahukuntan ƙasar da su dakatad da shirinsu na sarrafa sinadarin yureniyum.

Shugaban tawagar Iran a kan batun makamshin nukiliyan, Ali Larijani, ya faɗa wa maneman labarai cewa, shawarar na ƙunshe da wasu matakai masu ma’ana, waɗanda kuma ya kamata a yii cikakken nazari a kansu. Ali Larijani ya yi wannan jawabin ne, bayan da babban jami’in kula da harkokin ƙetare na Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, Javier Solana, ya gabatar wa mahukuntan birnin Teheran wani shiri na tallafa wa Iran ɗin a huskar cinikayya da kuma fasahohin ƙere-ƙere.

Shugaba Bush na Amirka, ya yi marhabin da amsar da Iran ta bayar ga wannan tayin, inda kuma ya nanata shirin ƙasarsa na shiga shawarwari da Jumhuriyar Islaman, idan ta dakatad da duk ayyukan sarrafa sinadarin yureniyum. Tayin dai, wanda ba a bayyana duk abin da ya ƙunsa ba, na kuma ɗauke da wasu matakai na ladabtad da Iran ɗin, idan ta ƙi ba da haɗin kai ga shawarwarin.

Ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter-Steinmeier, ya kyautata zaton cewa, Iran za ta ba da cikakkiyar amsa ga tayin, kafin a fara taron ƙoli na ƙasashen rukunin G-8 a ran 28 ga wannan watan a ƙasar Rasha.