1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta nada sabon kwamandan Sojojoji

Abdul-raheem Hassan
January 3, 2020

Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya nada Esma'il Qaani a matsayin sabon kwamandan sojojin juyin-juya halin kasar bayan da wani harin sojojin Amirka ya halaka Qassem Soleimani a Bagadaza.

https://p.dw.com/p/3VgXG
Iran Ayatollah Ali Khamenei, Oberster Religionsführer
Hoto: Reuters/Leader.ir

Gwamnatin Iran ta sha alwashin daukar fansa a kan Amirka biyo bayan harin jiragen yakin Amirkan da ya yi sanadiyyar rasuwar babban kwamandan sojojin juyin-juya halin kasar ta Iran Qassem Soleimani a filin jirgin Bagadaza babban birnin kasar Iraki.

Hari ta sama da sojojin Amirkan suka kaddamar dai, umurni ne daga Shugaba Donald Trump da zimmar murkushe Iran daga yunkurin kai hare-hare a kan muradun Amirkan a yankin Gabas ta Tsakiya.

Masu aiko da rahotanni daga Tehran babban birnin kasar Iran na cewa, dubban 'yan kasar sun bazama kan tituna suna Allah wadai kan matakin Amirkan na kashe Soleimani.

Manyan kasashen duniya ciki har da Jamus na shawartar Amirka da ta dakatar da kai hare-haren, dan takaita tashin wutar jeji tsakaninta da Iran.