Iran ta dage akan matakin ta
September 22, 2006Daya daga cikin manya manyan malamai a Iran , wato Akbar Hashemi Rafsanjani yace Iran ba zata dakatar da matakin ta na ci gaba da sarrafa sanadarin Uranium ba.
A cewar malamin, sharuddan da kasashe masu fada aji suka gindayawa kasar , don kawo karshen rikicin nukiliya, abubuwa ne da ba masu karbuwa ba.
Malamin wanda yake daya daga cikin masu bawa shugabann addini na kasar shawara, ya fadi hakan ne, a lokacin da yake jawabi ga masallata a masallacin jami´´ar Tehran a yau juma´ar nan.
Idan dai za´a iya tunawa , shugaba Bush na Amurka yace dakatar da sarrafa sadarin Uranium na daga cikin sharuddan komawa teburin sulhu da kasar ta Iran.
A cikin jawabin daya gabatar a gaban babban taron Mdd a jiya, shugaba Mahmud Ahmadinajad, yace kasar sa a shirye take ta warware rikicin nukiliyar ta, amma idan an sa adalci a ciki.