Iran ta dakatar da shigo da alkama daga ketare
May 9, 2024Talla
Mahukuntan na Iran suka ce a tsakanin watan Maris na shekarar da ta gabata zuwa watan Maris na wannan shekara, manoman kasar sun noma alkama ton miliyan 10.5, abin da ya sanya su yin odar ton miliyan daya kadai daga waje.
La'akari da wannan nasara, gwamnatin ta Iran ta ce ba ta sa ran za bude kofar shigo da alkama a kasar har sai watan Maris na shekara ta 2025, inda za ta duba kwazon manoman kasar wanda shi ne zai haska mata fitilar shigo da alkamar daga ketare ko kuma a'a.
A shekarun baya Iran ta rika wadatar da kanta a noman alkama, sai dai rashin samun ruwan sama a wasu shekarun kan kawo mata cikas.