Iran ta gargadi kasashen yammaci adangane da kai mata hari
September 22, 2007Iran tayi gargadin cewar,kasashen yammaci na turai zasu nadaman,ko wane yunkurin afkawa Tehran da harin soji,adangane da harkokinta na Nuclear.Shugaban kasar Mahmoud Ahmedinejad yayi wannan furucin ne,dayake jawabinsa na shekara shekara wa dakarun kasar ,bayan sun gudanar da Paredi,inda kuma aka kaddamar da sabon makami mai linzami,mai zuwa dogon zango.Ya bayyana cewar wadanda ke zaton zasuyi karan tsaye wa cigaban Iran,ta hanyar kakaba mata takunkumi na tattalin arziki ,da barazanar kai mata hari ,sunyi babban kuskure.Wadannan kalamai na shugaba Ahmedinejad dai sunzo ne,yini guda bayanda manyan kasashen duniya suka gudanar da tattaunawar,kara kakabawa Tehran din takunkumi,saboda kin watsi da shirin nuclearnta.A yau nedai shugaban na Iran yabar kasarsa zuwa halartan zauren mdd a birnin New York,inda kae saran zaiyi jawabi.