1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta gargaɗi Izraela kan harin ta wa Siriya

February 4, 2013

Sakataren majalisar ƙolin Iran ya ce zata yi amfani da kujerarta na shugabancin ƙungiyar ƙasashen 'yan baruwanmu wajen mayar da martani a madadin Siriya.

https://p.dw.com/p/17XjJ
Hoto: picture-alliance/dpa

Iran ta faɗa wa Izraela cewar, za ta yi nadamar harin da ta kai wa Siriya ta sararin samaniya a makon da ya gabata. Sakataren majalisar ƙoli mai kula da sha'anin tsaro na ƙasar Saeed Jalili, ya sanar da hakan wa taron manema labaru a birnin Damaskus, yini guda bayan tattaunawarsa da shugaba Bashar al- Assad. Jalili ya danganta harin da Izraela ta kai a sansanin sojoji dake yankin arewa maso yammacin Damaskus a ranar larabar data gabata, da rigingimun baya, da suka haɗar da yaƙin kwanaki 34 da ƙungiyar Shi'a ta Hezbollah a 2006. A cewarsa, duk waɗannan yaƙe yaƙe ne da Izraela ta yi nadamar gudanar da su. Sakataren majalisar ƙoli mai kula sha'anin tsaro a Iran ya ce, ƙasarsa za ta yi martani a madadin Siriya, a matsayinta na jagorar ƙungiyar ƙasashen 'yan ba ruwanmu. A ranar lahadin nan ce dai ministan tsaron Izraela Ehud Barak, ya bayyana harin da suka kai wa sansanin ajiyar makaman na Siriya da cewar, yana daga matakan da Izraela ke ɗauka na kare kwararar makamai zuwa cikin Lebanon. Wannan dai shine karon farko da Izraela ta yi amana da kai hari ta sararin samaniya.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe